Najeriya za ta kara kudi a fannin tsaro | Labarai | DW | 14.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya za ta kara kudi a fannin tsaro

Babban akantan kasar ya sanar da cewar a asusun rarar man fetur na Najeriyar na makare da zunzurutun kudi sama da dala biliyan biyu

Zentralbank von Nigeria

 

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya shaida wa manema labarai a Abuja babban birnin kasar cewar, yabawar da gwamnonin kasar suka yi  da irin cigaban da aka samu a bangaren yaki da Ta'addanci, shi ne dalilinsu na amincewa da a fidda dala biliyan daya daga asusun don cigaba da yakar ayyukan ta'addanci a kasar.

An  dai tsayar da lokacin sabon zaben shugaban kasa da gwamnaonin Najeriya a watan Fabarairu zuwa watan Maris na shekara ta 2019,lamarin da tarihin ya nuna shike zaburar da 'yan siyasa wajen satar kudaden kasar.