Najeriya: ′Yan bindiga sun kora mutane Nijar | BATUTUWA | DW | 14.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: 'Yan bindiga sun kora mutane Nijar

Sama da 'yan gudun hijira 2,000 ne suka shigo a garin dan Kano da sauran garuruwa na kan iyakar Maradi da Zamfara da sabon birnin Sokoto.

Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko (Getty Images/AFP/S. Heunis)

Al'ummar jihohin Zamfara da Sokoto na tserewa zuwa Nijar

'Yan gudun hijirar dai na isa garuruwan kan iyaka Nijar da Najeriya, irinsu  Dan Kano da Nakuka dan tsira da rayukansu daga barazanar 'yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a yankin. 'Yan gudun hijirar dai sun samu tarbo na karamci daga jama'ar garuruwan da suka sauka, inda aka basu wuraren kwana na wucin gadi. Tuni dai hukumar kula da 'yan gudun hijira reshen jihar ta Maradi suka kai ziyarar gani da ido domin tantance girman matasalar. A fili take dai akwai bukatar kawo agajin gaggawa domin a taimaka musu. Kawo yanzu dai jama'ar garuruwan da 'yan gudun hijirar suka sauka ne ke ci gaba da daukar dawainiyarsu kafin gwamnati da masu hannu da shuni su yunkuro.

Sauti da bidiyo akan labarin