Taron zaman lafiya a jihar Plateau
January 31, 2023Mahalarta taron na Jos sun tautauna ne game da batutuwa da suka shafi hadin kan al'ummar kasa da batun babban zabe mai zuwa tare da jaddada bukatar ganin jama'a sun fita zaben domin zabar shugabannin na kwarai ba tare da nuna bambancin siyasa ko addini ba. Reverand Moses Jatau Ebuga babban sakataren Mujami'ar TEKAN a Najeriya, guda ne daga mahalarta taron. A cewarsa al'ummar Najeriya sun sha fama da wahalhalu da dama sakamakon rashin zaman lafiya da fahimtar juna a lokaci irin wannan, a dangane da haka ya kamata su farga.
Taron ya gudana ne karkashin kungiyar Fastoci ta arewacin Najeriya, kuma wakilai daga kungiyoyin addinin Musulumci da na Kirsta dabam-dabam sun hallara, inda suka tabo batun matsalar tsaro da kuma na nuna bangaranci cikin siyasa tare da yadda wasu al'umma ke nuna siyasar kabilanci da ma bambancin addini. Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya da shugabanin al'ummomi dabam-dabam, inda suka tautauna game da fa'idar samun shugabanci na gari tsakanin al'ummar kasa. Cif Doughlas Echachala shugaban al'umma ne na 'yan kabilar Igide da ke jihar Benue ya ce ya kamata gwamnati ta rika shirya irin wadannan taruka domin samun hadin kan al'ummar kasa. Mahalarta taron sunci alwashin isar da manufofin tabbatar da zaman lafiya a lokaci da kuma bayan babban zaben kasar da ke tafe.