1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya : Zaman zulumi bayan hari a Filato

Abdullahi Maidawa Kurgwi AMA
November 29, 2021

An tura karin jami'an kwantar da tarzoma a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/43XQB
Nigeria Abuja | Sicherheitspersonal | Entführte Studenten
Jami'an tsaron Najeriya na kokarin tabbatar da doka da odaHoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

Mazauna  kauyen Tegwe dake gundumar Miango cikin karamar hukumar Bassa, sun sheda wa DW cewar maharan sun auka wa yankin ne da tsakar daren wannan Alhamis, inda suka yi ta kone-konen gidaje, kafin daga binsani lamarin ya kai ga kisan mutane 10 acewar wani basaraken yankin da ya nemi a sakaye sunan sa. "Ya ce mutane na kwance a gidajensu sai ga mahara da misalin karfe daya na dare, bayan sun kone gidaje sun kuma kashe mutane 10, yanzu haka akwai jami'an tsaro kuma an fara zaman makoki." 

An shiga halin zullumi a yankin, sakamakon yadda  mazauna kauyen ke nuna dan yatsa kan Fulani makiyaya da zargin cewa sune suka kai harin, zargin da Umar Abdullahi Dakare, shugaban kungiyar miyetti Allah kautal-hore na yankin karamar Bassa ya karya ta. "Ya ce ba Fulani gabadaya a garin, domin da akwai Fulani da an gansu, idan wani ya kai hari sai a zargi Fulani."

Karikatur Nigeria Ethnische Krise
Hoton barkwanci

Karin Bayani : Karfin sojoji ya kusa kare wa a Najeriya

Wanan hari na zuwa ne bayan da jihar Filato ta sami zaman lafiya  a yan watanin baya, inda ta shafe dogon lokaci ba tare da fuskantar  wani tashin hankali ba, koda yake an shafe shekaru ana samun tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin na Bassa, don haka masharhanta irin su Shaaibu Zakari Lamba ke cewar yakamata gwamnatin Filato ta kafa sansanonin jami'an tsaro a karamar Bassa don shawo kan lamarin yana cewa. "Wannan karamar hukuma na fama da matsalolin tashe-tashen hankula a nan shawararmu ita ce a kafa rundunar tsaro kamar yadda ake da ita a nan birnin Jos dan hakan zai taimaka a samu sauki."

Duk kokari da DW ta yi don samun karin bayani daga jami'an tsaro game da sabon harin na Bassa lamarin yaci tura, to sai dai wata majiya ta tabbatar mana da cewar rundunar dake wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta tura jamai'anta a yankin na Miango dake karamar ta Bassa don tabbatar da doka da oda.