Najeriya ta magance cutar Ebola | Siyasa | DW | 20.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta magance cutar Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta tabbatar da cewa Najeriya ta shawo kan cutar Ebola mai saurin kisa da wani dan kasar Laberiya ya kai mata tsaraba, kuma a yanzu babu burbushin cutar a kasar.

Babban wakilin hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Dr Rui Gama Vaz ne ya wanke sunan Tarayyar Najeriyar daga jerin kasashen da ke fama da annobar cutar Ebolan mai saurin kisa a wani bikin da ya samu halartar masu ruwa da tsaki na harkokin lafiyar kasar dama wajenta.

Wannan dai na zaman babbar nasara ga Tarayyar Najeriyar da ta sha fama da annobar Ebola inda akalla mutane bakwai suka kai ga barzahu cikin 12 da suka kamu da cutar tun farkon bullarta kasar a cikin watan Julin da ya gabata.

Shirin Layukan kotakwana a kan Ebola a Najeriya

Shirin Layukan kotakwana a kan Ebola a Najeriya

Kwanaki 42 babu rahoton cutar

Bayan kwashe kwanaki 42 ba tare da samun rahoton bullar cutar a fadin Tarayyar Najeriyar ba, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta yanke hukuncin wanke sunan kasar wanda ya mayar da ita ta farko a cikin yankin na yammacin Afirka da tai nasarar shawo kan matsalar. An dai sha biki da Owambe a tsakanin ma'aikatan lafiyar kasar da ke kallon shawo kan na Ebola a matsayin babbar nasarar da babu irin ta a cikin tsarin da ke tafiyar kwan-gaba-kwan-baya na lokaci mai tsawo.

Magance Ebola ya daga darajar kasar

Jami'an lafiya da matakan kariyar kamuwa da Ebola

Jami'an lafiya da matakan kariyar kamuwa da Ebola

Dr Khalliru Alhassan dai na zaman karamin ministan lafiyar kuma ya ce ranar na zaman ta farin ciki ga daukacin kasar da ma shugabannin da suka jagoranci yakin da ya daga darajar sunan kasar a tsakanin 'yan uwanta na duniya.

To sai dai kuma a yayin da kasar ta Najeriya ke tsallen murnar ganin bayan cutar ta Ebola dai, daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya ga kokarin kare cutar baki daya da ga shigowa cikin kasar da makwabtanta ke tsaka a cikin kogin annobar. Dr Nasiru Sani Gwarzo dai na zaman shugaban kwamitin tabbatar da hana shigowar cutar ta kan iyakoki na kasar, kuma a fadarsa gwamnatin kasar na shirye da nufin ganin ba'a sake samun satar shiga da Ebola zuwa Najeriyar ta makwabta ba.

Sauti da bidiyo akan labarin