1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta karyata biyan kudin fansar daliban Neja

Abdul-raheem Hassan
February 25, 2026

Hukumomin Najeriya sun karyata zargin biyan mayakan Boko Haram kudin fansar daliban makarantar sakadare da aka sace a jihar Neja.

https://p.dw.com/p/59MKJ
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola TinubuHoto: Sarah Meyssonnier/Pool Photo via AP/picture alliance

Gwamnatin Najeriyar ta musanta zargin ne bayan kamfanbin dillacin labarai na AFP ya wallafa rahoton bincike kan cewa jami'an gwamnati sun biya ''makudan'' kudade a matsayin fansa na sake daliban makarantar St. Mary's Catholic Church da ke kauyen Papiri fiye da 260 da aka sace a watan Nuwamban 2025. AFP ya ce gwamnati ta yi musanyar wasu kwamandojin kungiyar da ke tsare.

Wata sanarwa da ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris Malagi ya fitar a ranar talata, ya ce zargin AFP ba gaskiya ba ne.

''Gwamnati na jaddada cewa tuhume-tumen da rahoton ya bayyana, zuki ta malle da aka tsara don raba kan 'yan kasa'' inji sanarwar ministan yada labaran Najeriya.

Sai dai rahoton da kamfanin dillancin labaran na AFP ya wallafa, ya dogara ne kan hujjojin da ta samu daga majiyoyi masu karfi, amma gwamnatin Najeriyar ta ce ba za ta lamunci hujjojin da aka yi amfani da su ba saboda ba a bayyana ko suwaye ne su ba.

Sace daliban makarantar kwana ta St. Mary na daya daga cikin manyan garkuwa da dalibai da aka yi a Najeriya, inda satar mutane don neman kudin fansa ta zama gama-gari ga kungiyoyi masu dauke da makamai na samun kudi cikin gaggawa a kasar mai yawan mutane sama da miliyan 200 kuma ke fama da rikici .