1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A karon farko NNPC ya kafa tarihi cikin shekaru 44

August 27, 2021

Babban kamfanin man Najeriya NNPC ya baiyana samun ribar da ta kai ta kusan Naira miliyan dubu 300 a karon farko cikin shekaru 44 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3zaZB
BG Regierungssitze | Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Tun daga shekarar 1977 da gwamnatin Najeriya ta kafa NNPC  da nufin tafi da harkokin man kasar kamfanin na karewa da asara duk da dubban miliyoyi na dalolin da yake sarafawa a cikin harkar man a duk shekara, alal misali kamfanin ya yi asarar da ta kai dalar Amirka miliyan dubu 18 a tsakanin 2011 ya zuwa 2013, kana kuma ko a shekarar 2018 kadai kamfanin ya kirga asarar da ta kai Naira miliyan dubu 800 sakamakon kasa biyan kudaden danyen man daya diba da kuma tallafin tattacen da yan kasar ke sha a farashi mai rahusa.

Karin Bayani: Makomar masana'antar man fetur a Najeriya

A karon farko kamfanin NNPC ya aiyana samun ribar da ta kai Naira miliyan dubu 287 bayan daukacin harajin da gwamnatin kasar ta karba hannunsa da rage kisan kudin tafi da kamfanin da kusan kaso 30 a cikin dari game kuma da rage tsomin bakin yan mulki na kasar wanda ya taimaka wajen sabon yanayin daya burge ita kanta Abujar da shugaban kasar ya yi shelar ribar dake zaman sabon sauyi a cikin harka kamfanin man Najeriya.

Ölgewinnung in Afrika - Symbolbild
Hoto: picture-alliance/A. Holt

Wannan ribar na zuwa ne kasa da tsawon makonni biyu da rattaba hannu bisa dokar masana'antar man fetur da ta tanadi yancin tafi da harkokin kamfanin anan gaba. Ko da yake a fadar Engineer Muhammed Lawal dake zaman daya a cikin ma'aikatan hukumar dake kula da harkoki na kamfanin man fetur cewa "Tun ma kafin dokar, matakin dauke ragama ga masu fada ajin bangaren Abujar ga kamfanin ya sanya NNPC riba har a cikin annoba ta corona."

Karin Bayani: Kudirin dokar fasalin man fetur a Najeriya

Idan har kamfanin yana tsallen murnar sauyi, daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya a tsakanin NNPC da yan uwansa irinsu Saudi Aramco dake kasar Saudiyya ko kuma Petrobras na Brazil. A cikin watan Yuli ne kamfanin ya baiyana kashe tsabar kudi har dalar Amirka miliyan dubu biyu da dari bakwai da nufin sayen kaso 20 cikin dari na matatar mai ta Dangote dake shirin farin aiki a farko na badi.