Najeriya: Sojoji na neman baki da aka sace | Labarai | DW | 18.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sojoji na neman baki da aka sace

Hukumomin tsaro a Tarayyar Najeriya sun baza jami'an tsaro a cikin daji domin neman Amirkawa biyu da 'yan kasar Kanada biyu da aka sace da yammacin ranar Talata kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Nigeria Soldaten (AP)

Dakarun sojin Najeriya

Mutanen hudu 'yan kasashen wajen an sace su ne a kan hanyarsu ta zuwa Abuja bayan da suka taso daga garin Kafanchan a cikin jihar Kaduna, inda wasu mutane dauke da makammai suka sace su bayan da suka kashe 'yan sanda biyu da ke yi wa bakin rakiya kusa da Jere bisa hanyar Kaduna zuwa Abuja wurin da ake yawan fuskantar matsalar sace-sacen mutane.

Wani babban jami'in sojan na Najeriya da bai so a bayyana sunan shi ba, ya ce suna bisa kan wannan aiki na neman mutanen kuma tuni sun soma cin nasara kan wannan bincike.