1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan rundunar tsaro ta mata zalla

Uwais Abubakar Idris RGB
July 22, 2021

Najeriya ta samar da runduna ta mata zalla domin kare makarantun kasar daga hare-haren masu garkuwa da dalibai don neman kudin fansa.

https://p.dw.com/p/3xsIq
Nigeria Abuja | Sicherheitspersonal | Entführte Studenten
Hoto: Nasu Bori/AFP/Getty Images

A Najeriya fara tura rundunar da ke bada kariya ga farar hula ta mata zalla domin kare makarantun daga matsalar masu kai hare-hare da garkuwa da dalibai, ya sanya maida martani a kan tasirin da wannan zai iya yi a kokari na kare makarantun daga wannan matsala da ta kama hanyar sake durkusar da tsarin ilimin boko. Karin Bayani:  Rashin tsaro da makomar ilimi a Najeriya

Wannan runduna ta mata zalla, sun samu horo na musamman ne kafin turasu zuwa makarantun Najeriya a sassa dabam-dabam domin kawar da tsoro ta hanyar samar da tsaro a makarantun da suka zama wurare na baya-bayan nan da masu kai hare-haren, suka mayar wurin da suka kutsa kai cikin sauki, su dauki dalibai su yi awon gaba da su. 

Symbolbild Entführungen von Frauen und Mädchen in Nigeria
Sace 'yan matan Chibok ya haifar da gangamin Bring Back Our GirlsHoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Tura mata zalla na rundunar Najeriyar mai samar da kariya ga farara hula, sabon salo ne a kasar a kokari na kyautata yanayin tsaro. Ilimin boko ya shiga mawuyacin hali musamman a yankin arewacin Najeriyar tun daga shekarar 2014 da aka fara samun wannan matsala lokacin da aka kwashe ‘yan mata a makarantar sakandaren Chibok, inda bayan nan abin ya ci gaba da ta’zara a kasar da ke da yara sama da milyan goma.

Karin Bayani:  Sakin 'yan matan Chibok 21: Nasara ga gwamnatin Najeriya

Duka wannan matakin da ya biyo bayan nasarar da aka gani bayan tura sojoji mata zalla a hanyar Kaduna da aka samu sauki sosai a kan matsalar garkuwa da jama’a a hanyar. Najeriya na kokari na sake farfado da shirin samar da tsaro a makarantun kasar da tun bayan kwashe 'yan makaranta Chibok da aka yi da farko aka kafa shi bisa tallafin tsohon Firaiministan Birtaniyya.