Najeriya ta fitar da sunayen 'yan Chibok da suka tsira
May 8, 2017Talla
Mahukuntan Najeriyar sun fidda sunayen ne bayan ganawar da shugaba Buhari ya yi da su da yammacin jiya Lahadi, inda daga bisani ya mike birnin Landan na Birtaniya don sake bibiyar lafiyarsa.
Iyayen yaran na Chibok dai na cike da zumudin ganin 'ya'yan na su da suka dauki shekaru uku cur a dajin Sambisa, babbar tunga ta mayakan na tarzoma. 'Yan Najeriya masu yawa na ta zagaya runfunan jaridun kasar don ganin sunayen 'yan matan da suka tsira.
Tuni ma dai wasu daga cikin iyayen 'yan matan suka kasance a Abuja fadar gwamnatin kasar a kokarin ganin 'ya'yan na su. Jami'an na Najeriyar dai sun ce an yi musayar 'yan matan da kwamandoji biyar na Boko Haram, da dama ke tsare.