Najeriya: Kotu ta ce Buhari ya ci zaben 2019 | Siyasa | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kotu ta ce Buhari ya ci zaben 2019

Bayan share awa kusan tara kotun zaben shugaban kasa a Najeriya ta kori karar da dan takarar jam'iyyar PDP na adawa Atiku Abubakar ya shigar na neman kotun ta soke zaben shugaban kasar na 2019.

Sama da watanni shida bayan zaben gama garin da aka yi a Najeriya kotun da ke sauraron karan zabe ta tabbatar da zabin da aka yi wa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a wa'adi na biyu na mulki a shekara ta 2019. Babban alkalin kotun Muhammed Garba ya yi watsi da karan da jam'iyyar adawa ta Atiku Abubakar ta shigar na cewar a soke zaben saboda zargin da ta yi na magudi. A zaben dai da aka gudanar a watanni shidan da suka wuce Muhammad Buhari shi ya samu nasara da kishi 56% yayin da Atiku Abubakar ya samu kishi 41%.

Sauti da bidiyo akan labarin