1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kara karfin aljihun 'yan siyasar Najeriya

October 26, 2022

Yayin da ake fama da rikicin rashin kudi da mummunan talauci, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana shirin sake nazarin albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar.

https://p.dw.com/p/4IixN
Najeriya | Muhammadu Buhari | Talauci
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Ubale Musa/DW

Kama daga shi kansa shugaban kasar ya zuwa karamin kansila a gunduma dai, kusan duk wani mai rike da mukamin siyasa na shanawa a Tarayyar Najeriyar. Kuma a yayin da mafi karancin albashin ma'aikata ya fara daga Naira dubu 30, a wata dai kusan kowanne a matakai na jihohi da ma ita kanta tarayyar na zuwa gida da tsakanin naira dubu 500 zuwa miliyan a wata da sunan alabashin da alawus din aiki. To sai dai kuma Hukumar Kula da Albashin Masu Rike da Mukaman Siyasa a kasar, ta ce za tai nazari da nufin karin albashin da ya dauki shekara da shekaru da kuma hukumomin ke tunanin ya gama aiki. Shekaru 14 da suka gabata ne hukumar ta yi karin na karshe ga 'yan siyasar kasar, kuma ta ce tana shirin sake masa duban tsaf da nufin dacewa da zamanin.

Najeriya | Muhammadu Buhari | Talauci
Karin albashin 'yan siyasar Najeriya, cikin dimbin matsaloli da tarin bashiHoto: DW/A. Baba Aminu

To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba, matakin ya fara jawo daga hakarkari cikin kasar. Abbayo Nuhu Toro dai na zaman sakataren kungiyar TUC, ta manyan ma'aikata na gwamnatin Najeriya da ya ce sabon karin ya saba da hankali da tunanin 'yan kasar. Kokari na babba bisa karami, ko kuma adalci kan kowa in har ma'aikata na ganin ba daidai, ga masu rike da mukamin na siyasa batun da ke kasaya wuce batu na 'yan uwa da iyalai. Jika zuciyar abokan taku ko kuma wakaci ka tashi dai, an dai dauki lokaci ana ayyana 'yan dokar Najeriyar da zama na kan gaba a bangaren albashi a duniya. To sai dai kuma abun da suke karbar dai bai taka kara ya kai ga karyawa ba, a fadar Inusa Abubakar da ke zaman dan majalisar wakila a Najeriyar. Batu na karin albashin da alawus a cikin karin fatara da talauci dai, na zaman gaba cikin rikicin da ya kai dogon yajin aiki na kungiyar malaman jami'o'in kasar wato ASUU. Kuma a fadar Dakta Isa Abdullahi da ke zaman wani malami a jami'ar Jos dai, akwai yiwuwar sabon rikici a cikin neman dadawa masu takama da siyasar.