1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP za ta tsayar da dan takara daga arewacin Naieriya

September 24, 2021

A cikin tsakiyar rigingimu da ma kace-nace, jam'iyyar PDP ta adawa a Najeriya ta ce ta yanke shawarar mai da kujerar shugabancinta zuwa kudancin kasar a wata alamar cewa za ta fid da dan takarar shugaban kasar a Arewa.

https://p.dw.com/p/40pBs
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Da ma dai an dauki lokaci ana ta hasashen yiwuwar PDP biko ga sashen arewacin tarrayar Najeriyar da a baya ya nuna adawa da yadda jam'iyyar ta kare shekaru 16 tana kisa tana shan romo, amma kuma aka kare da shekaru biyu kacal a bangaren na arewa.

Wani taron wani kwamitin da shugabancin jam'iyyar ya dora wa alhakin tantance sassan da za su fid da gwanayen da za su kai ga jagorantar jam'iyyar a mataki na shugabanci na kasa. Duk da cewar dai taron ya kare a duhu, kafafen labarai na kasar sun ce kwamitin a karkashi na gwamnan Enugu ya kare tare da yanke hukunci mayar da shugabancin jam'iyyar ya zuwa Kudu maso yammacin kasar a yayin kuma da sakatarenta zai fito daga sashe na arewa.

An dai yamutsa gashin baki a tsakanin masu tunanin shugabancin jam'iyyar ya juya zuwa arewacin kasar da kuma masu neman da ya zauna a Kudu kafin kaiwa ga hukuncin da 'yan lemar ke shirin su fitar bainar jama'a nan gaba kadan.

Karin bayani: Sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya

Matakin a cikin al'ada dai na nufin jam'iyyar za ta fid da dan takara na shugaban kasa daga sashen arewacin kasar a yayin babban zabe na gaba. Matakin kuma da har ila yau ya dada rai na da dama da suke kallon damar arewacin kasar na samun mulki a cikin jam'iyyar.

Comrade Sa'idu Bello dai na zaman daya a cikin magoya bayan tsohon mataimakai na shugaban kasar Atiku Abubakar da ke neman sake takara ta shugaban kasar cikin PDP, kuma a fadarsa "PDP ta kyauta a kokari na ceto kasar da ke tangal-tangal a cikin mulki na masu tsintsiya."

Magoya bayan PDP a jihar Edo da ke kudancin Najeriya
Magoya bayan PDP a jihar Edo da ke kudancin NajeriyaHoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Koma ya zuwa ina 'yan lemar ke iya kaiwa a kokari na zawarcin na arewa dai, matakin dai ya harzuka bangarori da yawa a cikin jam'iyyar.

Karin bayani: PDP ta ce babu batun karba-karba a 2023

Kuma kama daga dattawan jam'iyyar da ke Kudu da ke neman damar mulkin, ya zuwa ga magoya bayan dakatacce na shugaban jam'iyyar Uche Secondus, 'yan jam'iyyar da dama sun ce sabo na matakin na kama da mafarkin rana da ba shi da tasiri ga makomar jam'iyyar.

Dr Umar Ardo dai na zaman daya a cikin masu goya baya ga Secondus, da kuma ya ke fadin sun nufi kotu da nufin neman rusa daukaci na hukuncin PDP.

Kokarin adalci kan kowa ko kuma neman hanyar huda laimar a cikin marka-marka, PDP dai na kara kusantar zabe a cikin tsananin rikicin da ke iya kara mata rauni a cikin tsananin rauni.

To sai dai kuma kokarin zawarcin na arewa daga dukkan alamu na iya tayar da hankali har a cikin APC mai mulki da ta share shekaru takwas a mulkin na arewa.