1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Inganta rayuwar mutanen da rikici ya shafa

February 14, 2024

Bayan share tsawon lokaci ana nunin kwanji, gwamnatin tarrayar Najeriya ta kaddamar da wani Shirin inganta rayuwar mutanen da rikicin makiyaya da manoma ya kassara a sashen arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4cP0u
Wani Bafulani Makiyayi a Jos Najeriya
Wani Bafulani Makiyayi a Jos NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Sabon Shirin na da babban burin kai kauce wa karfi da mai da kai zuwa ga kwakwalwa a cikin neman mafitar rikicin makiyaya da manoma a sashen arewacin kasar.

Akalla gidaje guda 1000 za'a gina a jihohin Katsina da Sokoto da Jihar Kebbi, Ko bayan Benue da Kaduna da Zamfara da jihar Niger a karkashin shirin da ke da fatan sauya tunani na kabilar Fulani.

Karin Bayani: Miyetti Allah: Mafita kan tsaro a Najeriya

Wani manomi a Jihar Sokoton Najeriya
Wani manomi a Jihar Sokoton NajeriyaHoto: Luis Tato/AFP

Abujar dai na kallon sabuwar dabarar da idanun mafitar rikicin na shekara da shekaru da ke zaman barazana mai girma a tsakanin al'umma.

A baya dai Abujar ta fuskanci adawa da wani shiri na samar da ruga ta zamani ga masu sana'ar kiwon da wasu ke yi wa kallon sana'ar da ke zaman ta masu neman riba.

Kuma ko yanzun daga dukkan alamu dabarar ta Pulako na shirin fuskantar adawa har cikin shugabannin kabilar ta Fulanin tarrayar Najeriya a halin yanzu.

Wani da aka kone gidansa a rikicin manoma da makiyaya a Kaduna
Wani da aka kone gidansa a rikicin manoma da makiyaya a KadunaHoto: AFP/Luis Tato

Dr Abubakar Umar Gire jigo a kungiyar Fulani ta kasar ya ce sabon shirin bai wuci kokarin sace zuciyar fulin Najeriyar ba.

Karin Bayani: Plateau: Magance rikicin manoma da makiyaya

Babu dai kasafin da ake shirin kashewa domin aikin da ake yi wa kallon an kusa makara a kasar da ke fuskantar karuwar rikici a tsakanin makiyaya da manoma.

Sai dai kuma a fadar Nasir idris gwamnan kebbi, jihohin da ke cikin shirin a halin yanzu, na da burin kai wa har karshe a kokarin samun zaman lafiya tsakanin makiyayan da kuma manoma.

Tarrayar Najeriyar dai na asarar adadin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 14 a shekara daga rikicin makiyaya da manoman da ke kan gaba a kasar a halin yanzu.