1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Babu tilas a shirin tsugunar da makiyaya

July 1, 2019

Duk da yunkurin samar da maslaha a rikicin makiyaya, gwamnati ta ce ba za ta tilasta wa kowacce jiha a game da sabon shirin Ruga na tsugunar da masu sana’ar kiwo ba.

https://p.dw.com/p/3LQKM
DW Fulani
Hoto: DW/K. Gänsler

Shirin na Ruga dai na da babban burin samar da wurare tare da gina ababen more rayuwa da zummar inganta sana’ar kiwo a wasu zabbabun wurare a cikin jihohin Najeriya. Kuma babban makasudinsa na zaman kai karshen kai kawon makiyayan da ake zargi da hannu a rikice-rikicen da ke lakume rayuka a cikin kasar a halin yanzu.

Polizei in Kano Nigeria
Kiwon dabbobi na fuskantar barazana a NajeriyaHoto: Imago/Zuma Press

Akalla jihohi goma sha biyu ne dai suka aiyana aniyarsu ta taka rawa cikin shirin a karon farko. To sai dai kuma tun ba’a kai ga ko’ina ba aka fara nunin yatsa a tsakani na jihohin da ke zargin gwamnatin kasar da kokari na kwace gonaki da nufin dadadawa makiyayan. Al’ummar Jihohi irin Benuwe  da ke yankin Arewa ta tsakiya da ma gwamnoni na daukacin jihohin Kudu maso gabas da naa yamma sun ce a kai kasuwa, shirin da acewarsu ke neman maida sana’ar kiwo hidima ta gwamnatin tarraya.

Ana dai kallo na siyasa cikin shirin da ke neman raba kan kasar tsakani na arewa dama kudu. Abun jira a gani dai, na zaman yadda take iya kayawa ga shirin da ke zaman dabarar karshe ga gwamnatin na kai karshen matsalar da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar a halin yanzu.