Najeriya: An dakatar da shirin RUGA | Labarai | DW | 03.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An dakatar da shirin RUGA

Bayan share tsawon kwanaki ana kace-nace kan shirin nan na RUGA a Najeriya wanda ya tanadi tsugunar da Fulani makiyaya a waje guda da ake son aiwatarwa, gwamnatin kasar ta sanar da dakatar da shirin.

Gwamnatin ta Najeriya ta ce ta dau matakin dakatar da shirin saboda irin cece-kucen da ake yi a kai. A wani zama da kwamitin nan na wadata kasar da abinci ya yi a Abuja, mukaddashin kwamitin kuma gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ce, Shugaban kasar Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin dakatar da shirin na RUGA. Ya bukaci da a sake duba shi da nufin yi masa gyaran da ya kamata, ta yadda wandada za su amfana da shirin za su ci moriyarsa sosai, sannan a kawar da duk wani abu daga cikinsa da ka iya jawo fitina a kasar.