1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Damuwa bayan sa hannu kan dokar zabe

February 19, 2026

A yayin da ake kara kusantar zabe a tarayyar Najeriya 'yan adawa da kungiyoyin sa ido na nuna damuwa kan rattaba hannu bisa sabuwar dokar zaben da ta jawo takkadama a kasar

https://p.dw.com/p/5966O
Taron shugabannin Jami'yyar APC mai mulkin Najeriya
Taron shugabannin Jami'yyar APC mai mulkin NajeriyaHoto: Presidencia Villa Abuja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu bai bata lokaci ba wajen rattaba hannu kan dokar zaben, duk da damuwa ta adawar da kwarrarun dake kallon tsarin zaben kasar suka nuna

Doka ta biyu mafi daukar hankali a Najeriya bayan dokar haraji da gwamnatin kasar ta gabatar a shekarar 2025

Tinubun da ya sa kafa ya shure zanga zangar masu adawa da damuwa ta kungiyoyin farar hula na da jan aikin daukar kasar zuwa babban zabe a cikin tunanin adalci.

Adalcin da daga dukkan alamu ke nuna raguwa a tunanin masu adawar da ke shirin goga kafada da kila kokarin kare mulki na masu tsintsiyar.

Koma ya zuwa ina masu adawar ke shirin su kai a kokarin biyan bukata, daga dukkan alamu mafi daukar hankali cikin neman sauyi na zaman tasirin zaben cikin fasahar zamani, ko kuma a'a.

An dai dauki lokaci ana bugawa tsakanin masu mulkin da ke fadin suna shirin yin dai dai, da kuma masu adawar da ke fadin da sauran sake.

To sai dai kuma ana bukatar Imanin yan kasar a harkar mulki kan sauyin da yan kasar ke bukata yanzu, a tunanin Bala Ibrahim jigo a jam'iyyar APC mai mulki.

Adalci cikin batun zaben, ko kuma wayon a ci, an kori kare daga gindin dinya, kace-nacen da ke cikin gidan siyasar na zuwa ne shekara guda da tabbatar da sabon shugaban tarayyar Najeriyar.

Najeriyar dai na dada nisa a kokarin samar da shugabanni ga kasar amma a cikin halin rudu da kallon kallo.