Najeriya: Daliban sakandare za su rubuta jarabawar WAEC | Labarai | DW | 27.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Daliban sakandare za su rubuta jarabawar WAEC

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin a sake bude makarantun kasar don bai wa daliban makarantar Sakandare da ke a ajin karshe damar rubuta jarabawarsu ta WAEC, a yayin da kasar ke ci gaba da yakar annobar Corona.

Ga yadda lamura suke a sassan duniya a game da annobar Coronavirus. Babban mai bai wa shugaban Kasar Amurka shawara kan tsaro Robert  O'Brien ya kamu da cutar Coronavirus, sai dai bayanai daga fadar White House na cewa, Shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence ba sa cikin hadarin kamuwa da cutar.

Kasashen yankin Turai kuwa, na fuskantar sabbin kalubale bayan da aka soma samun karuwar yaduwar cutar. A kasashen Spaniya da Jamus da kuma Beljiyum, alkaluman masu kamuwa da cutar sun karu, makonni kadan da soma bude wuraren yawon bude ido, lamarin da ake ganin na son mayar da hannun agogo baya a nasarar da aka samu kan annobar.

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin bude makarantu don bai wa daliban makarantar Sakandare da ke a ajin karshe damar rubuta jarabawarsu ta WAEC, daga ranar biyar ga watan Augusta mai kamawa daliban za su koma makaranta a yayin da ake sa ran su rubuta jarabawar, a ranar sha bakwai ga watan goben.

A baya can an yi zatan daliban ba za su sami damar zana jarabawar ba, bayan da gwamnati ta baiyana damuwarta a saboda karuwar yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

A kasar Kenya da ke yankin kahon Afirka, gwamnati ta kara tsawaita dokar hana fitan dare na wata guda, kadan ya rage Shugaba Uhurru Kenyatta ya kara rufe kasar a sakamakon yadda cutar ke kara yaduwa, yanzu haka an haramta sayar da barasa a duk fadin kasar. Cutar ta riga ta halaka mutum sama da dari biyu da hamsin tun bayan bullarta a Kenya. Covid-19 ta kama mutum sama da miliyan goma sha shida a fadin duniya. Ana dai daba da samar da allurar riga-kafin cutar da ta zame ma duniya alakakai.