Najeriya: Buhari zai je London don duba lafiyarsa | Labarai | DW | 08.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Buhari zai je London don duba lafiyarsa

A wannan Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi birnin London na kasar Britaniya, inda zai gana da likitan da zai duba lafiyarsa kamar yadda ya sanarwa 'yan kasa a yammancin ranar Litinin.

Buhari mai shekaru 75 bai yi karin bayani kan lafiyar ta sa ba. Sai dai ba wannan ne karon farko da yake zuwa birnin London kan batun lafiya ba, don kuwa a bara ma ya shafe fiye da wata guda ya na jinya a wani asibitin kasar Britaniyan kan cutar da ba a baiyana wa jama'a ba.

Tuni masu sharhi suka soma tsokaci da cewa, wannan batu ka iya haifar da damuwa kan koshin lafiyar shugaban da ke da niyyar sake tsayawa takara a babban zabe na shekarar 2019.