1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Hare-haren karshen shekara

December 28, 2018

Mayakan Boko Haram sun kai wasu jerin hare-hare a wasu garuruwa da ke jihohin Borno da Yobe.

https://p.dw.com/p/3Ak2l
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Boko Haram na ci gaba da yin kisaHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Garuruwan da mayakan na Boko Haram suka kai harin na baya-bayan nan dai sun hadar da Goniri da Gruwa a karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe da kuma Doron Baga da Croos Kauwa da Kukawa a jihar Borno, inda su ka fadada yankunan da suke iko da su a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar. Mayakan Boko Haram da ake alakantawa da kungiyar ISIS mai neman kafa daular Musulunci a nahiyar Afirka ta Yamma na zafafa kai hare-haren kan sansanonin jami’an tsaro a jihohin Borno da Yobe abin da ake ganin wani kokari ne na fadada yankunan da su ke iko da su. Yanzu haka mayakan na Boko Haram sun karbe iko da shalkwatar rundunar hadin gwiwa ta kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi wato MJFT, wadanda ke muhimmin gari na Baga da ke karamar hukumar Kukuwa a jihar Borno.

Boko Haram sun kafa tutoci

Symbolbild Flagge Boko Haram
Boko Haram sun kafa tutoci a wasu garuruwa Hoto: Getty Images/AFP/S. Yas

Shaidun gani da ido da su ka gudo daga yankunan sun tabbatar da cewa mayakan na Boko Haram sun kafa tutocinsu, kuma su ne ke jan sallah a masallatai a garin na Baga wanda ke kan iyakokin kasashen da ke bakin gabar Tafkin Chadi. Wani bawan Allah da ya fito daga garin Baga da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya tabbatar da cewa ya ga jami’an tsaron Najeriya na guduwa, mayakan Boko Haram din kuma na iko da garin. Rundunar sojoji dai ta tabbatar da hare-haren da aka kai da ta ce sun ma rasa jami’in sojan ruwa daya a harin Baga sai dai sun ce sun dakile hare-haren gami da musanta maganar cewa an karbe iko da yankunan. Masharhanta dai sun nemi hukumomi su tashi tsaye domin magance wannan matsalar da ke mayar da hannun agogo baya ga nasarori da ake ikirarin an samu a yaki da Boko Haram din.