Najeriya: Bikin baje kolin litattafai a Lagos | Zamantakewa | DW | 29.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: Bikin baje kolin litattafai a Lagos

A Najeriya an gudanar da bikin baje kolin litattafan marubutan Afirka da aka yi wa lakabi da Ake a birnin Lagos inda aka gabatar da litattafai da aka rubuta kan maudu'ai da suka shafi rayuwar Afirka ta da da ta yanzu.

Flash-Galerie MC Lagos Bücher

A Najeriya, harkar rubuce-rubuce da wallafe-wallafen litattafai ta bunkasa sosai a cikin 'yan shekarun baya-bayannan. A yanzu ma yawancin marubuta suna dukufa kan al'amuran siyasa tare da karkata kan abubuwan da suka gabata kamar bauta da mulkin mallaka. Wannan ya fito fili ne yayin bikin litattafai da ake yi wa lakabi da Ake a Lagos.

Logan Febraury ya yi amfani da littafin da ya fitar mai taken in the Nude wajen sosa inda yake yi wa dimbin al'umma kaikayi. Wannan dalili mai shekaru 20 da haihuwa wanda kuma ka rayuwa a Lagos yana daga cikin marubuta da suke tabo batun neman jinsi a cikin litattafansu. Dama akwai litattafai da dama a 'yan shekarun nan da suka mayar da hankali a kan wannan batu kama daga na marubuci Chinelo Pkparanta ya zuwa na Olumide Poppola. Logan febraury na daukar adabi a matsayin wata kafa ta sauya tunanin al'umma, kasancewa har yanzu duk wanda aka samu da laifin luwadi ko madigo za a iya aiwatar masa da hukuncvin daurin shekaru 14 a gidan yari, ga kuma batun launin fata wanda Logan ya yi tsokaci a kai:

"Bakin jiki na kunshe da sakon siyasa, lamarin da ke sa shi bakar fata farko. A matsayinmu na mutane, dukkaninmu muna da jiki, wannan shi ne dalilin da ya sa ya kamata mu bar duk abubuwan da ke raba kawunanmu. Tunda muna magana ne game da bambancin launin fata da kabilanci a yanzu, mu da muke bakar fata dole ne mu yi magana game da kalar fatarmu domin ba a wanann batun ya zuwa  yanzu."

Bunkasa da rubutun adabi ya yi a nahiyar Afirka ta ba da damar tabo al'amuran da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya, tare ma haifar da muhawara kan muhimman batutuwa kamar bauta, shekaru 400 bayan dibar wasu bakaken fata daga Afirka zuwa Amirka don aiki a gonaki. Sannan kuma mulkin mallaka a kasashen Afirka da zamantakewar al'umma da al'adunsu bayan samun 'yancin kai suma sun kasance a cikin tattauna da aka yi a bikin adabi na Ake na birnin Lagos. Lola Shoneyin da ta shirya bikin ta yi kira ga jama'a da su fito su amayar da abubuwan da ke damunsu a karkashin rubuce-rubuce:

"Littattafai da yawa na kasashen Afirka suna magana kan mahimman al'amuran zamantakewa da kuma al'amuran yau da kullum. Amma kuma suna waiwaye kan abin da ya gabata, wanda har yanzu ana jin tasirinsa . Hatta litattafan da ba su yi kama da na siyasa ba da farko suna da matukar taka rawa."


Litattafan da ke maida hankali kan matsalolin Afirka kuma wadanda 'yan Afirka ke rubutawa na dada karuwa a kowace shekara. Ko da a Najeriya an kafa masana'antar buga litattafai da yawa a cikin shekaru 20 da suka gabata irin su Kachifo Limited, da Cassava Republic da Ouida Books. Sannan marubutan adabi suna kara samun yabo daga kasashen duniya.  Bernadine Evaristo, wacce ta lashe kyautar Booker tare da hadin gwiwar Margaret Atwood a cikin shekarar nan ta 2019, ta ce yana da matukar muhimmanci a bayyana labarin mata bakar fata goma sha biyu a cikin littafinta mai taken "Girl, Women, Other". Sai dai Evaristo ta ce wata marubuciya 'yar kasar Amirka da ke da tushe da Najeriya ne gwanarta:

"Babban wadda na fi so ita ce Toni Morrison, marubuciya Ba'amirkiya, da take da salon rubuta  da ke matikar burge ni. Ta kasance abin koyi a gare ni, da ma sauran marubutan Amirka da ke da tushe da Afirka a lokacin da nake karama, saboda ba mu da wannan tsarin adabin a Birtaniya kwata-kwata."


Littattafan sun kuma ba da damar doguwar tattaunawa a kan kyamar baki da ta tayar da fitina tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya. Dama marubuci dan Najeriya Chika Unigwe, wanda sabon littafin yake da taken "Better never then late" ya yi fama da kalaman wariyar launin fata a Amirka inda yake rayuwa.