Najeriya: An sace ′yan mata a Yobe | Zamantakewa | DW | 22.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: An sace 'yan mata a Yobe

A Najeriya wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace 'yan mata sama da 90 a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabaashin kasar da kuma da ke fama da hare-haren ta'addanci.

Nigeria Boko Haram Terrorist (picture alliance/AP Photo)

Mayakan Boko Haram da suka addabi Najeriya da makwabtanta

Duk da cewa gwamnatin Tarayyar Najeriyar ta musanta zancen sace 'yan matan 'yan makarantar sakandare a jihar Yobe, sai dai mahukuntan jihar ta Yobe sun sanar da cewa jami'an tsaro sun fafata da mayakan na Boko Haram tare da ceto wasu daga cikin 'yan matan. A baya dai gwamnatin Tarayya Najeriya ta nunar da cewa sojojin kasar na samun nasara a yakin da suke da mayakan na Boko Haram da suka addabi Najeriyar dama wasu makwabtanta.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin