Najeriya: Sojojin sun kubutar da wasu dalibai | Labarai | DW | 22.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Sojojin sun kubutar da wasu dalibai

Sojoji a tarayyar Najeriya sun yi nasarar kubutar da wasu daga cikin daliban da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu a arewa Jihar Yobe gabashin kasar a jiya laraba.

An dai wayi gari da bacewar 'yan mata dalibai a makarantar 'yan mata ta kwana dake garin Dapchi a jihar Yobe a ranar litinin din da ta gabata wadanda kwamishinan ilimin jihar Muhd Lamin yace yawan su zai kai kimanin 50.

Sojojin kasar sun yi nasarar kwato 'yan matan da ga 'hannun 'yan ta'addan a garin Jilli-Muwarti dake kan iyakar jihar Borno da Yobe. Tun da fari dai shugaba Muhammadu Buhari ya ba rundunar Sojoji da 'yan sandan kasar umarnin su yi gaggawar nemo daliban.

Tun a shekara ta 2009 dai Kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da kai hare hare tare da yin garkuwa da mutane a arewa maso gabashin kasar duk da kokarin ganin kawo karshen ta'addanci da gwamnatin kasar ke cigaba da yi.