Najeriya: An kori Boko Haram daga Sambisa | Labarai | DW | 24.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An kori Boko Haram daga Sambisa

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce sojin kasar sun karbe iko da babbar maboyar 'yan kungiyar nan ta Boko Haram a cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno wadda a baya suka maida tungarsu.

A wata sanarwa da fadar Aso Rock ta fidda a dazu, an ambato Shugaba Buhari na cewar da misalin karfe 1 da mintuna 35 na ranar Juma'ar da ta gabata ce sojin na Najeriya suka karbe iko da wannan waje wanda hakan ya sanya mayakan na Boko Haram ranta a na kare. Shugaban na Najeriya ya ce da wannan nasara da dakarun kasar suka samu a iya cewa an kai mataki na karshe na murkushe kungiyar baki daya. Tuni dai rundunar sojin kasar ta bakin kakakinta Burgediya Janar Sani Usman Kukasheka ta bayyana gamsuwarsta da wannan aiki da dakarunta suka yi.