Najeriya: An fara shari′ar ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An fara shari'ar 'yan Boko Haram

A wannan Litinin din ce aka fara yi wa wasu 'yan kungiyar nan ta Boko Haram shari'a bisa zarginsu da ake yi da tada zaune a kasar musamman ma dai a yankin arewa maso gabas inda kungiyar ke tada kayar baya.

Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce za a yi wa mutanen shari'ar ce a asirce kuma za a fara da mutum 1,670  wadanda ake tsare da su a wani sansanin soji da ke Kainji a jihar Neja da ke tsakiyar kasar. Baya ga wannan, za a yi wasu mutanen 651 shari'a a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri na jihar Borno su din ma dai bisa zarginsu da hannu wajen tashin hankalin da kungiyar ta Boko Haram ta haddasa. Ministan shari'a Najeriya Abubakar Malami ya ce kowanne mutum da ake tuhuma na da 'yancin daukar lauyan da zai tsaya masa.