Najeriya: An ceto limaman coci da aka sace | Labarai | DW | 13.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An ceto limaman coci da aka sace

Hukumar 'yan sanda ta jihar Delta a Najeriya ta sanar da ceto limaman cocin Katolika guda hudu wadanda wasu 'yan bindiga suka sace a yankin Kudu maso gabashin kasar a makon da ya gabata. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wanda ya ruwaito babban kwamandan na 'yan sandar jihar Delta Muhammad Mustafa na cewa rukunin wasu jami'an 'yan sanda ne ya yi nasarar ceto limaman cocin a ranar Juma'ar da ta gabata a Abraka wani kauye na yankin Delta inda ya ce sun kama mutane da dama da ake zargin da hannu wajen sace limaman cocin. 

Kasa da makonni uku da suka gabata ma dai wasu 'yan bindigar sun sace a jihar ta Delta wasu mata hadiman cocin Katolika su biyar kafin su sako su bayan sun kwashe kwanaki 15 a hannunsu. A watan Janerun da ya gabata dai shugabannin coci a Najeriya sun soki lamirin yadda tabi'ar sace mutane domin neman kudin fansa ta zamo ruwa dare a kasar.