1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar RGB
July 30, 2021

Annobar corona da zazzabin malariya a kasashen nahiyar Afirka su suka dauki hankula a sharhunan da jaridun Jamus suka rubuta kan nahiyar a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3yKnO
Türkei Pfizer BioNTech Ampullen
Hoto: Abdurrahman Antakyali/Depo Photos/ABACAPRESS/picture alliance

Kamar yadda aka saba jaridun Jamus din wannan makon sun tabo batutuwa da dama da suka fi daukar hankali a kasashen mu na Afrika. Amma bari mu fara da batun corona. "Kasashen Afirka na bukatar nasu allurar rigakafi" da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta bude labarin da ta rubuta nai taken "CORONA".

Jaridar ta ci gaba da cewar, a 'yan kwanakin da suka gabata lamura sun kasance tamkar kamalallu ga Afirka. Shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai Ursula von der Leyern ta sanar da babban labari kan nahiyar.Ta gabatar da yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kamfanin BioNtech da Biovac na Afirka ta Kudu. Kamfanonin biyu na muradin sarrafa allurar sanfurin BioNtech a Afrika ta Kudun.

Impfkampagne in Südafrika
Afirka na fuskantar karancin riga-kafin coronaHoto: Siphiwe Sibeko/AP Photo/picture alliance

Kafofin yada labaru sun yayata wannan labari na farin ciki, 'yan siyasa sun yaba da wannan yarjejeniya a matsayin muhimmin ci gaba  na adalci wajen samar da allurar wa duniya baki daya. Sai dai idan an yi nazari sosai, "sarrafawa" na nufin zuba maganin cikin kwalabe kadai. Amma kamar yadda aka sani rawar ba za ta sauya ba.

Kamar sauran shugabannin kasashe marasa galihu, Shugaba Cyril Ramaposa ya nemi manyan kamfanonin sarrafa magunguna su soke 'yanci mallaka, domin bai wa kanana damar yin allurar da kansu. Duk da cewar kusan a Afirka aka yi gwajin dukkan alluran riga-kafin, ya zuwa yanzu ana iya cewar babu gajiyar da al'umma suka samu, hasali ma har yanzu Afirkar ce a baya idan aka zo batun riga-kafin.

Malaria-Bekämpfung in Afrika | Kenia | Impfstoff Mosquirix
Malariya na halaka kananan yaraHoto: Brian ONGORO/AFP

Daga batun corona sai yaki da ta'addanci a yankin Sahel. Jaridar Die Tageszeitung ta ce bayan shekaru takwas na yakar ayyukan ta'addanci a Mali da sauran kasashe makwabta na yankin Sahel, Faransa ta fara janye dakarunta.Kungiyoyin 'yan ta'adda na kara yin karfi, kuma bisa dukkan alamu lamarin na neman ya gagari kundila a cewar jaridar. Sai dai duk da haka Shugaba Macron ba shi da wani zabi face ya janye sojojinsa.

Janye sojojin na zama sabuwar dabarar shugaban na Faransa na yaki da ayyukan ta'addanci. A karkashin tsarin dai, rundunar Faransar da ake kira Barkane da ke yakar kungiyoyin ta'adda a kasashen Mali daNijar da Burkina Faso tun 2014, da aka kara yawansu zuwa 5,100 kusan shekaru biyu da suka gabata, za a rage yawansu zuwa rabi nan da 2023.

Kuma Shugaba Macron ya jaddada wannan batu a taron da yayi da shugabannin kasashen na Sahel a Paris a ranar 9 ga watan Yuli. Faransar za ta rufe sansanoninta da ke Kidal da Timbuktu da Tessalit da ke arewacin Mali, tare da mika wa rundunar hadakar MDD ta MINUSMA a karshen shekara.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, sharhi ta rubuta mai taken "BioNTech na yaki da Malaria". Jaridar ta ce, da cizon macen sauro daya, mutum na iya kamuwa da zazzabin Malaria. Inda aka kiyasta cewar a shekara ta 2019 kadai, mutane miliyan 229 suka kamu da cutar. 

Malaria cuta ce da idan har an gano ta da wuri, mutum zai iya samun waraka. Amma duk da haka hukumar kula da lafiya ta MDD watau WHO ta kiyasta mace macen mutum dubu 409 a 2019, daga zazzabin cizon sauron. A kasashen Afirka ne aka fi fama da Malaria, kuma ta fi hadari ga kananan yara wadanda shekarunsu bai shige biyar ba. Uku daga cikin Hudun mace macen na Malariya na daga wannan rukuni na yara.

Tsawon shekaru kenan kamfanoni da cibiyoyin bincike da gidauniyoyi da hukumomi ke fafutukar neman bakin zaren yakar wannan cuta da ta yi kaka-gida a Afirka. A yanzu kuma kamfanin sarrafa allurar rigakafi na BioNTech da ke birnin Mainz na Jamus, shi ma ya hade a wannan fafutuka.

A ranar Litinin da ta gabata ne, aka sanar da shirin manufar kamfanin na sarrafa allurar rigakafin zazzabin Malariyar a taron manema labaru da ya samu halartar wakilan WHO da hukumar gudanarwar Turai da gidauniyar Bill Gates da makamantansu, a karkashin shirin nan na kawar da Malaria a doron kasa.