Mutane sun mutu a hare-haren Maiduguri | Labarai | DW | 16.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sun mutu a hare-haren Maiduguri

Hukumomi a Najeriya sun ce hare-haren da 'yan kunar bakin wake da aka kai birnin Maiduguri sun halaka mutane sama da goma yayin da wasu da dama kuma suka jikata.

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu jerin hare-haren da 'yan kunar bakin wake hudu suka kaddamar a birnin Maiduguri, sun halaka mutane akalla 18 yayin da wasu 29 suka jikata. Shaidu sun ce harin na yammacin ranar Laraba, ya kasance cikin mafiya muni da aka gani a birnin a bana.

Kakakin rundunar kakakin jami'an 'yan sanda a Borno, Victor Isukwu, ya ce maharan maza biyu mata biyu, sun afka wa wani waje ne mai yawan masu hada-hada a 'Muna Garage'. Harin na farko a cewar 'yan sandan an kaddamar da shi a wani wajen da mutane ke Salla, kuma maharan hudu sun mutu.

Hare-haren dai na zuwa ne yayin da rahotanni daga yankin Madagali dake arewacin jihar Adamawa ma ke tabbatar da wani harin na Boko Haram a yankin da yammacin na Laraba.