Mutane da dama sun rasu a harin birnin Maiduguri. | Labarai | DW | 04.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun rasu a harin birnin Maiduguri.

Adadin mutanen da suka rasu a harin kunar bakin waken da aka Kai a birnin Maiduguri, ya kai na mutune 18 yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

A yammacin jiya Laraba wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani garejin gyaran motoci da ke kallon wani barakin soja a birnin na Maiduguri inda kanikawa da dama suka rasu. A kokarin da ya ke na ganin bayan rikicin kungiyar Boko Haram, sabon Shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari ya kai wata ziyara a kasar Nijar, inda ya tattauna da hukumomin kasar kan batun na tsaro a jiya Laraba.

A wannan Alhamis din kuma shugaban na Najeriya ya isa a birnin Ndjamena na kasar Chadi, inda ya Ghana da takwaransa na wannan kasa Idriss Deby da sojojin kasarsa ke taka rawa a yakin da ake da 'yan kungiyar ta Boko Haram. Ana sa ran daukan wasu sabin matakan yaki da 'yan kungiyar ta Boko haram nan bada jimawa ba.