Mutane 80 sun kubuta daga Boko Haram | Labarai | DW | 21.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 80 sun kubuta daga Boko Haram

Kanal Usman da ke magana da yawun sojan Najeriya ya ce dakarunsu sun aika mayakan na Boko Haram 42 lahira yayin da suka kubutar da yara da mata.

Nigeria Flüchtlingslager Flüchtlinge Kinder

Dubban al'umma ne dai maza da mata mayakan na Boko Haram ke garkuwa da su

Dakarun sojan Najeriya sun bayyana cewa sun sami dama ta kubutar da mutane 80 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a wani yanki da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Mai magana da yawun dakarun sojan na Najeriya Kanal Sani Kukasheka Usman ya bayyana haka inda ya ce a ranar Talata ce mutanen suka sami dama ta kubuta bayan da dakarun sojan na Najeriya suka yi barin wuta kan mayakan na Boko Haram a garin Gangare na jihar Borno.

Kanal Usman ya ce dakarunsu sun aika mayakan na Boko Haram 42 lahira yayin da suka kubutar da yara 42 da mata 38 daga hannun mayakan.

Sojojin na Najeriya dai sun bayyana kubutar da mutane daga hannun mayakan na Boko Haram sama da 10,000 a wannan shekara sai dai har yanzu yara 'yan makarantar Chibok 219 da aka kama tun a shekarar 2014 ba a kai ga kubutar da su ba.