Murar Tsuntsaye A Turai | Siyasa | DW | 15.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Murar Tsuntsaye A Turai

Cutar murar tsuntsaye ta fara rutsawa da kasashen KTT

Murar tsuntsaye a Turai

Murar tsuntsaye a Turai

Har dai ya zuwa halin da ake ciki yanzun dai cutar ta murar tsuntsaye ba ta rutsa da kaji da sauran dangin tsuntsaye da mutane ke amfani da su yau da kullum a kasashen Kungiyar Tarayyar turai ba, amma tuni akan gano kwayoyin cutar ta H5N1 a tsakanin tsuntsaye gangin balbela da ragowarsu. A sakamakon haka hukumar zartaswa ta kuma mahukunta na kasashenta suka tashin tsaye wajen gabatar da matakan da zasu taimaka wajen hana yaduwarta domin ta rutsa da dangin tsuntsayen da mutane ke kiwatawa a gida. An an shigence yankunan da tsuntsayen daji masu zirga-zirga tsakanin kasashe kan ya da zango a cikinsu a bakin koguna a tazarar kilomita uku tare da tilasta barin kaji aa agwagi da talotalo da makamantansu a akurki. Bugu da kari kuma da zarar an kwaso dabbobin za a zarce da su ne kai tsaye zuwa mayanka. Kazalika an haramta farautar tsuntsayen daji a tazarar kilomita goma daga yankunan da mutane ke zama. Bayan da cutar ta murar tsuntsaye ta rutsa da kasashen Girka da Italiya a karshen makon da ya gabata, a yanzun ta shigo nan Jamus da kasashen Austriya da Sloveniya da kuma Hungry. An saurara daga Kantoman hukumar zartaswa ta KTT Markos Kyprianou yana mai bayanin cewar a halin da ake ciki yanzun ba wani dalili na shiga wani hali na rudu da rashin sanin tabbas:

Ko da yake akwai yiwuwar barkewar cutar a wani gidan gona, amma ba zamu yi wata-wata ba wajen daukar matakai na gaggawa wajen magance ta gaba daya. A sakamakon haka ba wani dalili na fadawa cikin rudami. Kamata yayi mutane su kwantar da hankalinsu. Ko da cutar ta billa zamu yi bakin kokarinmu wajen shawo kanta.

A matakanta na tinkarar cutar tuni kungiyar tarayyar Turai ta haramta cinikin gashin kaza sannan ta ware karin kudi na Euro miliyan biyu domin tafiyar da ayyukan gwaje-gwaje a kasashenta. Kuma ko nda yake ita kaza idan an dafata ta ji wuta sosai kwayar cutar ba ta da wani tasiri a cikinta, amma tuni aka samu koma bayan cinikin sauran abubuwan da ake sarrafa su daga naman kaji daga kasashen da cutar ta rutsa da su kamar Girka da Italiya. A kuma halin da ake ciki kasashen Jamus da Netherlands da wasu kasashe na KTT na shirin haramta kiwon kaji da agwagi a waje sai dai a akurki kawai. Wasu kwararrun kiwon lafiyar dabbobi na kungiyar sun hallara a Brussels domin nazarin karin matakan kariya da za a dauka bisa manufa kamar dai kone kajin a yankunan da lamarin ya shafa. Kawo yanzu babu wani bayani a game da kamuwar dan-Adam da kwayar cutar a kasashen KTT, ko da yake a Turkiyya cutar ta halaka mutane hudu a cikin watan oktoban da ya gabata.