1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar harshen uwa ta duniya

Abdullahi Maidawa Kurgwi LMJ
February 21, 2024

Ranar harshen uwa ta duniya, rana ce da Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ware domin fadakar da mutane game da muhimmancin harsuna da al'adu mabambanta.

https://p.dw.com/p/4chmm
Harshen Uwa | Majalisar Dinkin Duniya | UNESCO
Muhimmancin harshen uwaHoto: Google

Ana dai fuskantar matsaloli da dama, sakamakon yadda wasu manyan harsuna kan mamaye kanana har ya kai ga bacewar su a bayan kasa. Ana alakanta wadannan matsalolin da yadda wasu kabilu kan yi watsi da harshensu na gado, tare da rungumar wanda ba nasu ba. Jihohin Plateau da Taraba da wani bangare na jihar Kaduna  da ke Tarayyar Najeriya, na daga cikin jihohi da ke da manya da kananan kabilu dabam-dabam. Ga misali a jihar Plateau bincike ya nuna akwai kabilu fiye da 40 wadanda ke magana da harsunansu, to amma sakamakon yadda wasu kabilun  ke watsi da nasu harsunan na asali wasu manyan harsuna na kokarin mamaye. Wannan ya janyo wasu kananan harsuna na neman bacewa, don haka Hukumar UNESCO ke bayar da muhimmanci ga wannan rana ta harshen uwa domin gudun bacewar kananan harsunan a duniya.