UNESCO hukumar kula da ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wadda take kula da abubuwa na tarihi a duniya da bunkasa su.
Hukumar wadda take da mazauni a birnin Paris na kasar Faransa tana kuma saka ido a wuraren da ake rikicin domin kare kayan tarihin da suke yi. An kirkiro hukumar a watan Nowamba na shekarar 1945.