1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harsunan gwari na fuskantar barazanar bacewa

Mohammad Nasiru Awal AMA
March 5, 2019

Kananan harsunan na fama da matsin lamba a Najeriya, sakamakon yadda harshen Hausa ke danne wasu harsunann gwari, a wuraren harkokin yau da kullum kamar kasuwanni da wuraren ibadu da gidajen biki.

https://p.dw.com/p/3ETcs
DW African Roots- Bayajida
Hoto: Comic Republic

A kowace ranar Alhamis ta 21 ga watan Fabrairu na shekara akan gudanar da bikin ranar harshen uwa kamar yadda hukumar ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta ware. Sai dai a wasu kasashen kamar a Najeriya na fuskantar barazana daga harshen Hausa wanda ke kan gaba wajan hadiye sauran kananan harsuna. Bacewar harsunan kananan kabilun na zama daya daga cikin abubuwan da ke janyo nakasu ga harkokin al'adun gargajiya na wadanna kabilun ko da yake a cewar wani dan gwagwarmayar kare al'adun gargajiya a Najeriya Steven Achi na kungiyar Pan-African Leadership League wannan matsalar da sakaci daga bangaren iyaye. Yanzu hakan harshen Hausa ya danne sauran harsunan kananan kabilun Najeriya, wanda bai bar kasuwanni da wuraren ibadu da gidajen biki da sauran wuraren tarurruka ba, kuma harshen shi ne harshen da kabilu dabam-daban ke anfani da shi wajan gudanar da harkokin su na yau da kullum. Domin ganin sun magance wannan matsalar tuni wasu kabilu suka fara daukar matakai na gudanar da bukukuwan sauran al'adunsu a kowane lokaci, tare da koyawa 'ya'yansu sauran wasannin gargajiya don kare al'dunsu daga barazanar bacewa daga doron kasa.