MTN kamfani ne na sadarwa na wayar salulu da ke da cibiyarsa a Afirka ta Kudu sai dai ya na da rassa a kasashe da dama a ciki da wajen Afirka.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da kamfanin ke da abokan hulda da damar gaske. A kwanakin baya kamfanin ya shiga matsala da hukumomin Najeriya bayan da aka ci tararsa ta miliyoyin daloli sakamakon kin bin wani umarni da hukumar sadarwa kasar ta bada na rufe layukan wanda ba su yi rijista ba.