Buhari ne zai yanke hukunci kan MTN | Labarai | DW | 26.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ne zai yanke hukunci kan MTN

Mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana cewar shugaban Najeriya ne ke da ikon yanke hukunci na karshe kan batun tarar da hukumar sadarwa ta yi wa kamfanin sadarwar MTN.

Masana harkokin sadarwar a kasar dai na ganin wannan tarar ita ce irin ta ta farko da hukumar sadarwar kasar ta sanyawa wani kamfanin sadarwa a Najeriya, daya kasa cika ka'idojin da hukumar ta gindaya masa.

Ana dai tuhumar kamfanin MTN din ne da laifin kin soke wasu layuka kimanin sama da miliyan biyar ga 'yan Najeriya wanda daga bisani suka fuskanci fushin hukumar sadarwar kasar.

A ranar alhamis din nan ce dai Tajudeen Kareem daga ma'aikatar harkokin yada labaran Najeriya yace shugaban kasar Najeriya nan gaba kadan ne zai yanke hukuncin karshe kan tarar da ake yiwa kamfanin MTN din.