Farmakin ramuwa kan MTN | Labarai | DW | 23.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farmakin ramuwa kan MTN

A Najeriya masu zanga-zanga sun auka wa ofishin wayar salaula na MTN da ke Abuja don ramuwa  bisa kashe 'yan Najeriya da aka yi a kasar Afirka ta Kudu yayin rikicin kyamar baki.

Kakakin MTN a Najeriya ya fadawa manema labarai cewa, mutanen suna zanga-zanga ne kan hallaka 'yan Najeriya wanda zauna gari banza masu gyamar baki suka yi a Afirka ta Kudu. Farmakin an kai shi ne a ofishin MTN da ke Abuja wanda, shi ne babban cibiyar sayarda layin salau na kamfanin a kasashen Yammacin Afirka da kuma ofishin hulda da jama'a na MNT. A cewar kakakin na MTN, wadanda suka kai farmakin sun lalata na'u'rorin kamfanin, kana suka sace wayoyin salula na kwastomini da ke cikin ofishin a lokacin da masu boren suka shiga.