Afirka ta Kudu za ta shiga tsakani a rikicin kamfanin MTN | Labarai | DW | 10.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu za ta shiga tsakani a rikicin kamfanin MTN

A karon farko gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce za ta shiga tsakani don shawo kan matsala a tsakanin Kamfanin sadarwa na MTN da gwamnatin Najeriya.

Tun a shekarar 2015 hukumar kula da harkar sadarwar Najeriya ta ci tarar kamfanin na kasar Afirka ta Kudu, don ta ki bin umarnin gwamnati na katse layukan jama'a miliyan biyar da ba su yi rijista ba. An yi ta kai ruwa rana a tsakanin bangarorin biyu sai dai yanzu kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya sami goyon bayan kasarsa da ke son ganin an warware wannan takaddama lami lafiya.

A can baya, gwamnatin Najeriya ta kakabawa kamfanin harajin dala biliyan biyu bayan da babban bankin kasar ya ci tarar kamfanin na kudi dala biliyan takwas.