Kamfanin sadarwa na MTN zai samu dan sararawa daga tarar da Najeriya ta ci shi | Labarai | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamfanin sadarwa na MTN zai samu dan sararawa daga tarar da Najeriya ta ci shi

Katafaren kamfanin sadarwa a Afirka wato MTN zai samu sauki daga tarar miliyoyin dubbai na dalar Amirka da hukumar sadarwar Najeriya ta ci shi.

Südafrika Sifiso Dabengwa

Sifiso Dabengwa shugaban MTN da ya yi murabus

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN a Afirka ya yi nasarar samun sararawa daga tarar da Najeriya ta ci shi ta dalar Amirka miliyan dubu 5.2, inda yanzu haka kamfanin zai samu damar tattaunawa don samun mafita. Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta ci kamfanin na MTN da ke zama mafi girma a harkar sadarwa a nahiyar Afirka, wannan tara bayan ya gaza toshe katunan waya miliyan 5.1 da ba a yi rajistarsu ba, abin da ya janyo faduwar hannayen jarin kamfanin da kuma tilasta shugabanta Sifiso Dabengwa yin murabus. A wannan Litinin wa'adin da hukumar NCC ta ba wa kamfanin ya cika, amma an jiyo kamfanin na MTN na cewa hukumar NCC ta amince da ka da a biya tarar har sai an kammala tattaunawar tsakanin bangarorin guda biyu.