MOD.: YADDA WASAN KARSHE YA KASANCE NA CIN KOFIN KWALLON KAFAR NAHIYAR AFRICA A TUNISIA: | Siyasa | DW | 14.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MOD.: YADDA WASAN KARSHE YA KASANCE NA CIN KOFIN KWALLON KAFAR NAHIYAR AFRICA A TUNISIA:

Kamar yadda masu sauraro kuka kwana da sani a yammacin yau asabar ne aka buga wasan karshe na neman cin kofin kwallon kafa na zinare na nahiyar Africa a tsakanin yan wasan kasar Tunisia dana kasar Morocco a can filin wasa na Rades dake kasar ta Tunisia.
To babu shakka wasa yayi wasa domin kuwa anyi gwagwagwa anyi kuma gumurzu a tsakanin yan wasan kasashen guda biyu. Mintuna kadan dai da fara wasan na karshe kasashen biyu suka dau dumi na kaiwa juna hare hare ba tare da samun nasara ba.
To amma kuma ana cikin haka ne dan wasan nan na kasar Brazil dake bugawa kasar Tunisia kwallo,wato Dos santos ya samu damar saka kwallo ta farko a ragar yan wasan kasar Morocco,bayan daya samu crossin din ball daga Mehdi Nafti.Hakan ya haifar da raye raye da tsalle tsalle tare da kara zuga yan wasan kasar ta Tunisia daga bangaren yan kallo na kasar da suka cika filin wasan na Rades. Bugu da kari a hannu guda kuma,ya karawa yan wasan kasar Morocco kwarin gwiwa na tashi tsaye domin neman saka kwallo ta farko a ragar gidan yan wasan na Tunisia.
Bisa kuwa ikon Allah a dai dai misalin mintuna 37 da fara wasan dan wasan kasar Morocco mai suna,Youssef Mokhtari ya samu damar jefa kwallo ta farko a ragar gidan yan wasan kasar ta Tunisia.
Jim kadan kuwa da farkewar yan wasan kasar ta Morocco wasa ya kara daukar wani sabon salo,a inda kowadanne yan wasa suka canja taku na kai hare hare da kuma tabbatar da tsaron gida da kyau,don kare abokan gaba kawo musu hari.
Wasa dai yaci gaba a haka a tsakanin yan wasannin bangarorin kasashen biyu,wanda a dai dai mintuna 47 da fara wasa Alkalin wasan daya kasance ya fito ne daga kasar Senegal ya hura busa ta kawo karshen zango na farko na wasan.
Bayan hutun mintuna goma sha biyar ne yan wasan suka dawo fagen fama domin ci gaba da fafatawa a tsakanin juna na raba raini dangane da fitar da kasar data cancanci daukar kofin zinaren na gasar wasan kwallon kafa na 24 na nahiyar ta Africa.
Rahotanni da suka iso mana sun shaidar da cewa wasa ya dauki tsafi mai tsananin gaske a yayin da aka shigo zango na biyu bayan yin hutun rabin lokacin.
Mintuna kuwa shida kacal da dawowa daga hutun rabin lokaci,dan wasan kasar Tunisia mai saye riga lamba biyar wato Ziad Jaziri ya samu damar kara jefa kwallo ta biyu a ragar yan wasa na kasar Morocco,bayan da ball ta subuce daga hannun mai tsaron Gida na kasar ta Morocco wato Khalid Fouhami.
Jim kadan bayan kara samun nasarar kasar ta Tunisia a karo na biyu,yan wasan kasar Morocco mike kain da nain wajen ganin sun samu galabar farkewa amma ina idan sun kai caffa sai a dawo dasu,haka suma yan wasan kasar ta Tunisia basu saki jiki ba domin kuwa suma sunyi ta kai hare hjaren neman kari amma abu yaci tura.
An dai ci gaba da wan nan yanayi har zuwa lokacin da Alkalin wasa ya hura busar tashi daga wasa,wanda a wan nan lokaci Kasar Tunisia nada kwalaye biyu ita kuma kasar Morocco nada kwaya daya kwalli.
Hakan ya bawa yan wasan kasar Tunisia,wacce daman itace take daukar bakuncin wasan nasara ta daukar kofin zinare na kwallon kafa na nahiyar ta Africa karo na 24. Ita kuma kasar Morocco ta zamo na biyu a inda yan wasan suka samu nasarar cin lambar Azurfa. Tarayyar Nigeria data zamo ta uku yan wasan kasar sun samu galabar tsira da lambar girma ta tagulla.
Kyaftin na kasar Tunisia Badra da dan wasa Bauzizi ne suka karbi kofin Zinaren tare da daga sahi sama a tsakanin dubbannin mutane a filin wasan na Rades dake kasar ta tunisia. Yin hakan kuwa keda wuya filin ya kaure da raye raye da wake wake na murnar samun nasasar yan wasan na Tunisia daga dubbannin yan kallo da suka samu galabar shogowa filin wasan na rades.
Rahotanni dai sun shaidar da cewa a yayin gabzawar yan wasan bangarorin duka sun nuna kwazo da kokari iya iyawarsu,to amma fitattu daga bangaren kasar Tunisia sun hadar da Riad Bauazizi da Ziad Jaziri da kuma Dos santos.daga bangaren kasar Morocco kuwa akwai dan wasa Yussef Hadji da Yussef Mokhtari da kuma Marouane chammakh.
A hannu daya kuma kamar yadda masu sauraro kuka kwana da sani a jiya juma,a ne yan wasan kasar Nigeria dana kasar Mali suka fafata da juna don neman matsayi na uku a gasar wasan kwallon kafar na nahiyar ta Africa karo na 24.
A takaice dai wasa ya kare a tsakanin kasashen biyu da suka fito daga yammacin nahiyar ta Africa,Nigeria nada kwallo biyu mali kuma nada guda daya,wanda hakan ya bawa Nigeria matsayi na uku kamar yadda muka shaida muku a baya.
A baya dai tarayyar Nigeria ta shigo wannan wasan ne da zummar komawa da kofin na zinariya izuwa gida to amma sai mai duka yayin nufin su da komawa gida da matsayi na uku.To amma kuma duk da haka kyaftin na Nigeria wato Jay jay Okocha yace yayi murna kwarai da gaske na samun wan nan matsayi na uku da kasar tasa tayi domin hakan a cewar sa yafi su koma gida babu komai. Kuma babban wani abuma daya kara faran ta musu rai shine na fitar da yan wasan Kamaru da sukayi daga dairar wasan,wanda hakan ya tilas ta musu komawa gida.