Ministocin kudin kasashen Turai za su gana kan kasar Girka | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin kudin kasashen Turai za su gana kan kasar Girka

Rashin bai wa kasar Girka kudaden da take bukata zai iya jefa kasar cikin rudadin tattalin arziki tare da fice daga kasashe masu amfani da kudin Euro

A wannan Alhamis ministocin kudin kasashen Turai ke ganawa a Luxembourg inda za su tattauna yuwuwar amincewa da bai wa kasar Girka kudade, domin ta kauce daga fadawa cikin matsalolin tattalin arziki.Wani rahoto daga babban bankin kasar ta Girka ya nuna cewa rashin samun kudaden zai jefa kasar cikin kasadar ficewa daga kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro.

A wani lokaci da safiyar wannan Alhamis ake sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fitar da sanarwa kan halin ceton tattalin arzikin kasar ta Girka.