Ministar tsaron Jamus tana shan suka | Labarai | DW | 03.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministar tsaron Jamus tana shan suka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna karfin gwiwa ga ministar tsaro Ursula von der Leyen bayan bankado zargi sojan da ya yi yunkurin kai harin matsanancin ra'ayi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana karfin gwiwa ga ministar tsaron kasar Ursula von der Leyen, bisa yanayin rudanin da aka shiga bayan bankado sojan da ake zargi yana neman kai hari irin na masu matsanancin ra'ayi. Mai magana da yawun shugabar gwamnatin ya tabbatar da haka.

Yanzu haka ministar tsaron ta Jamus Von der Leyen ta tafi garin Illkirch na Fransa domin ganin binciken da ake gudanar kan sojan da ake zargi, ya yi shigar burtu kamar dan gudun hijira. Ita dai ministar tsaron tana shan suka a cikin gida bisa yadda aka bankado wannan lamari na abin kunya.

Ursula von der Leyen ta zama ministar tsaron Jamus a shekara ta 2013 lokacin da shugabar gwamnati Angela Merkel ta gudanar da sauye-sauye cikin majalisar zartaswa.