Minisan cikin gidan Jamus ya gabatar da matakan dakile barazanar ta′addanci | Labarai | DW | 11.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Minisan cikin gidan Jamus ya gabatar da matakan dakile barazanar ta'addanci

Jamus za ta tsananta matakan ba sani ba sabo kan wadanda ake zargi ayyukan tarzoma da ke zama babbar barazana ga al'ummar Jamus.

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maizière ya kuduri aniyar daukar tsauraran matakan tsaro don dakile duk wata barazanar hare-haren ta'addanci a Jamus. Daga cikin matakan kamar yadda ministan ya sanar a birnin Berlin sun hada da tsananta sa ido kan baki da ke da alamun aikata laifuka da ake wa lakabi da masu hatsari ga kasa.

Ya ce: "Muna cikin wani lokaci mai hatsari. Barazanar ta'addanci ta kai kololuwa. Aikin ya yi wa 'yan sandar tarayya da na jihohi yawa. Gwamnatin tarayya da jihohi sun amince da daukar matakan ba sani ba sabo musamman wajen kai samame don riga-kafin duk wani hatsari ga al'umma."

A ranar Laraba jami'an tsaron Jamus sun kai samame a wasu wuraren kasuwanci da masallatai da ake zargi da tallafa wa 'yan tarzoma.