Mike Pompeo zai gana da Merkel | Labarai | DW | 01.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mike Pompeo zai gana da Merkel

Fadar gwamnatin Jamus ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo zai kaddamar da wata ziyarar aiki a birnin Berlin, inda zai gana da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da sauran kusoshin gwamnati.

Duk da yake sanarwar fadar gwamnatin ba ta fito fili ta fayyacce ko batun girka rundunar hadin gwiwa ta sojan kasa da kasa a arewacin Siriya na daga ciki jadawalin tattaunawar da za ta shiga tsakanin Pompeo da Merkel ba.

Rahotanni sun ce Sakatare Pompeo zai gana da wasu kusoshin gwamnatin Jamus ciki har da sakataren harkokin wajen Jamus Heiko Maas da ministar tsaro Annegret Kramp-Karrenbauer.