1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Merz: "A sanya Ukraine a matsayin kwarya-kwaryar mambar EU.

Mouhamadou Awal Balarabe
May 21, 2026

A matakin janta a jika kafin kammala tsarin shigo da ita cikin kungiyar EU, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya nemi a sanya Ukraine a matsayin "memba da ba na dindindin ba" a Kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/5E7PI
Shugaban gwamnatin Jamusr Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamusr Friedrich Merz Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A cikin wata wasika da ya aika wa shugabar hukumar zartarwa ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen da shugaban majalisar EU Antonio Costa, Merz ya nemi a amince wa manyan jami'an Ukraine da su rinka halartar taron koli na Kungiyar Tarayyar Turai da tarurrukan ministoci, amma ba tare da samun 'yancin kada kuri'a ba.

Karin bayani: Jamus: Tallafin makamai ga kasar Ukraine

Ukraine tana son shiga cikin kungiyar EU a matsayin wani mataki na neman karfafa tsaronta da wadata arzikinta sakamakon hare-haren da take fuskanta daga Rasha, ganin cewar har yanzu Amurka tana adawa da duk wani mataki na shigar da Ukraine cikin kungiyar tsaro ta  NATO.