Merkel zata ziyarci Turkiyya | Labarai | DW | 18.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel zata ziyarci Turkiyya

MERKEL

Shugabar gwamnatin Jamus mai jiran gado,Angela Merkel ta amince da gayyata da akayi mata zuwa turkiyya cikin watannin shidan farko na shekara mai zuwa,inda tayi fatan cewa kasashen biyu zasu ci gajiyar ingantacciyar dangantaka.

Angela Merkel tayi wannan furucin ne bayan ganawarta da ministan harkokin waje na Turkiyya Abdullah Gul,a birnin Berlin,wanda ya gabatar da wannan gayyata amadadin premier RecepTayyip Erdorgan.

Sabuwar shugaban gwamnatin tace tana fatan ganin kyakkyawar dangantakar hulda tsakanin jamus da turkiyya,musamman a matsayinsu na wakilan kungiyar tsaro ta NATO.

Jamus dai na mai zama gida na biyu wa baki turkawa,wadanda yawansu yakai million 2 da rabi a sassa daban daban na kasar.

Angela Merkel dai na daya daga cikin wadanda sukayi adawan shigar da Turkiyya kungiyar EU,batu dake kafa ayar tambaya dangane da huldodin kasashen biyu nan gaba.To sai dai jammiyar Merkel ta christian Democrates da kuma abokiyar hadin gwiwarta a gwamnati ta SPD dake marawa Turkiyyan baya,sun cimma matsaya guda kann batun a tattaunawa dasukayi a makon daya gabata.

A ranar talata nedai majalisar dokokin jamus zata zabi Angela Merkel,a matsayin mace ta farko da zata hau mukamin shugabar gwamnati a tasrihin jamus.

 • Kwanan wata 18.11.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7p
 • Kwanan wata 18.11.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7p