Merkel ta sassauta adawa da auren jinsi | Labarai | DW | 27.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta sassauta adawa da auren jinsi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sassauta adawarta da auren jinsi, matakin da ya farantawa yan luwadi da madigo da kuma ke zuwa yan watanni kafin zaben gama gari da za'a yi a jamus.

Da take jawabi bayan ganawa da 'yan jam'iyyarta, Merkel ta ce bujiro da auren jinsi batun ne da kowane dan majalisa zai duba a kan kansa bisa tunani na hankali da kuma yakinin da yake da shi kan batun domin yanke hukunci.

Jagoran gungungun yan jam'iyar ta CDU a majalisar dokokin ta Bundestag Volker Kauder ya yi kira ga dukkanin takwarorinsa su kada kuri'ar goyon baya ga kudirin. Yana mai cewa ya kamata wadanda ke adawa da auren jinsi, su martaba ra'ayin sauran al'umma.

Jagoran jam'iyyar adawa ta SPD da zai kalubalanci Merkel a zabe mai zuwa Martin Schulz yace zai bukaci majalisar ta kada kuri'a kan batun a cikin wannan makon.

A baya dai jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin ta sha nuna adawa da kin amincewa da aure tsakanin jinsi guda, wanda wasu manyan kasashen turai suka amince da shi a shekarun baya bayan nan.

Sauyin manufar dai na zuwa a daidai lokacin da kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna yawancin Jamusawa da sauran Jam'iyyun siyasa na goyon bayan bada dama ga aure tsakanin jinsi guda.