1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Merkel ta kadu da ta'asar ambaliya

Ramatu Garba Baba
July 18, 2021

Shugaba Angela Merkel ta bayyana kaduwa bayan gane ma idanunta irin ta'asar da ambaliyar ruwa ta haddasa a yayin da ta kai ziyarar gani da ido.

https://p.dw.com/p/3we6O
Deutschland  Unwetter in Rheinland-Pfalz | Malu Dreyer und Angela Merkel
Hoto: Christof Stache/dpa/AFP/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar yankunan kasar da iftila'in ambaliyar ruwa ya afkawa a wannan Lahadin. Merkel da ke wata ziyarar aiki a Amirka a lokacin iftala'in, ta kai ziyarar gani da ido a Schuld da ke yankin Ahrweiler, inda mutum 110 suka mutu a sakamakon ambaliyar a kauyen da al'umarsa ba su zarta 700 ba. Merkel ta baiyana kaduwa bayan gane ma idanunta ta'asar ambaliyar.

Tare da rakiyar gwamnan jihar Rhineland-Palatinate, Malu Dreyer da magajin garin na Schuld, Helmut Lussi sun tattauna da masu aikin ceto da kuma sauran jama'ar da matsalar ta shafa. A garin Erftstadt da ya fuskanci matsalar ambaliya mafi muni a tarihinsa, mutum kimanin 60 ne suka bata, a can jahar Bavariya da ke iyaka da kasar Ostiriya, an kwashe sama da mutane 100 daga gidajensu, a sakamakon ta'addin mamakon ruwan saman. Jimillar mutane 183 kawo yanzu, aka tabbatar da mutuwarsu sakamkon ambaliyar. Shugabar gwamnatin ta ce za a gaggauta wadata jama'a da duk irin tallafin da suke bukata kamar yada ta fadi a farkon makon nan.