Merkel na kokarin habaka danganta da AU | Siyasa | DW | 11.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel na kokarin habaka danganta da AU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara cibiyar kungiyar Tarayyar Afirka, wacce abokantaka ta sa a cikin shekaru goma, Jamus ta taimaka wa AU da Euro miliyan 500 don inganta zaman lafiya da tsaro a nahiyar.

Ana iya cewa wannan wata alama ce ta daddadiyar dangantakar da ta wanzu tsakanin Jamus da Kungiyar hadin kan Afirka tun bayan kafuwarta a shekarar 1963. A waje guda dai yayin da kasar China ta cika burin gina katafaren hedikwatar kungiyar hafin kan Afirka AU cikin kankanin lokaci, a daura da haka Jamus a nata bangaren na da wani kudiri muhimmi ga ginin wanda aka yi wa lakabi da ginin wanzar da zaman lafiya da tsaro na Julius Nyerere.

Na farko shi ne a shekarar 2014 da Jamus ta kawata ofisoshi 360 na ma'aikata a cibiyar AU da kuma babban zauren taro. Ko da karfafar dangantakar ta zo a makare ko kuma tarnaki daga bangaren kungiyar Afirka ta haifar da tsaiko, muhimmin al'amari shi ne a ranar Talatar nan 11 ga watan Oktoba an bude sabon babi na bunkasa dankon zumunci da ci gaba ta fuskar kulla wata sabuwar dangantaka a tsakaninsu ta kawancen ayyukan farar hula da na soji domin wanzar da zaman lafiya da tsaro wanda shugabar gwamnati ta wannan lokaci ta dabbaka.

Babban farin cikin shugabar gwamnatin shi ne samar da ingantaccen makamashi wanda Kungiyar Tarayyar Afirkar ta kaddamar a karshen shekarun 1990 tare da fatan bunkasa ci gaban nahiyar ta Afirka cikin hanzari.

A bangaren aikin wanzar da zaman lafiya, a 'yan shekarun baya-bayan nan, kungiyar ta gudanar da ayyuka da dama domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya. Alal misali kafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta AMISON a Somaliya. Judith Vorrath, kwararriya kuma mai nazari akan al'amuran siyasa ta ce kungiyar ta AU ta sami ci gaba ainun.

Afrika Kanzlerin Merkel in Äthiopien Einweihung Julius-Nyerere Gebäude für Frieden und Sicherheit (picture-alliance/dpa/M. Kappeler)

Ginin AU na zaman lafiya da tsaro da Jamus ta taimaka wajen ginashi

"Ta ce idan muka dubi bangarori kamar na diplomasiyya kungiyar ta yi rawar gani kuma an samu ci gaba"

Ita ma a nata bangaren Liesl Louw-Vaudran ta cibiyar nazarin al'amuran tsaro da ke birnin Pretoria a Afirka ta kudu, tsokaci ta yi tana mai cewa: "Kungiyar  AU ta samu ci gaba sosai, majalisar zaman lafiya ta tsaro ta kungiyar tana a matsayi ne tamkar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a daidai wannan lokaci. A nan ne ake zartar da galibin kudurori da kungiyar za ta aiwatar."

A dangane da kalubale da kungiyar ta AU ke fuskanta kuwa Liesl Louw-Vaudran cewa ta yi:

"Yana da matukar sarkakiya AU ta iya shiga tsakani a kasashen da ke daukar kansu a matsayin kasashe masu cin gashin kansu da kuma basa son ganin kungiyar ta AU a Addis Ababa ta rika yi musu katsalandan a harkokinsu na cikin gida. A saboda haka AU tana jan aiki na nuna cewa tana da karfin tasiri wajen tabbatar da zaman lafiya a Afirka da kare aukuwar rikice rikice "

A waje daya dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ja hankali dangane da ziyarar Merkel a Afirka da kuma kokarin fahimtar siyasar Jamus, nahiyar ta Afirka da kuma musamman manufofinta a kan batun 'yan gudun hijira.

 

Sauti da bidiyo akan labarin