Mayakan IS sun kashe sojojin Mali 35 | Labarai | DW | 02.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan IS sun kashe sojojin Mali 35

Wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, na cewa 'yan ta'addan sun yi wa dakarunta kwanton bauna a sansaninsu da ke arewacin kasar ta kan iyaka da Nijar.

Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar Mali na cewa adadin sojojin da suka mutu a harin ta'addancin ya kai 35. Wannan sabon hari na zuwa ne kasa da wata guda bayan wani hari da ya halaka sojojin Malin har 38 a wasu sansanoni biyu, arewaci da tsakiyar Mali na cikin tsaka mai wuya na hare-haren ta'addanci tun bullar 'yan aware a shekarar 2012.

Duk da cewa akwai sojojin hadin gwiwa da ke yakar ayyukan ta'addanci a kasar Mali, amma har yanzu 'yan bindiga na barazana ga rayuwar fararen hula da jami'an tsaro.